Mutane 350 Ne Suka Amfana Da Tallafin Mashin, Injin Markaɗe Da Atamfofi a Katsina
Daga Awwal Jibril 'Yankara
A Ranar Asabar 19/8/2023 Dan Majalisar Taraya Mai wakiltar kananan Hukumomin Kankara, Faskari Da Sabuwa a Majilisar Wakilai ta Kasa dake Abuja
Hon. Jamilu Mohammad Lion (Magayakin Faskari) yaraba Mashina da injin markade sama da guda 350 a garin Faskari karamar hukumar Faskari jihar Katsina
Dan Majalisar Taraya yayi kira ga Al'umma da suka Amfana da wannan kayan da suyi Amfani dashi ta hanyar data dace domin samun abin shiga
lokacin da yake raba kayan sana'ar ga Matasa da Mata Yayi kira ga wanda basu samu ba da suyi hakuri yanzu aka fara .
Daman a Ranar rantsar dashi a wata Yuli 13th 2023 Dan Majulisar Hon Jamilu Muhammad (Dan Zaki) Yi ma Matasa alkawarin tallafa masu su dogara da Kansu
wannan shine karo na 3 da yayi empowerment ga al'ummar Kananan Hukumin Kankara, Faskari da Sabuwa
Wadan da suka amfana sun sheda ma wakilil mu cewa wannan babban abin a yabane kuma babban abin alfahari ne ga Wannan yankin .
Baki Daya
Shugaban Jamiyar PDP Na Karamar Hukumar Sabuwa Hon. Aliyu Hasan ya yaba ma dan majalisar bisa irin Wannan na mijin kokari da ya yi na tallafa ma Mutane a irin Wannan Lokaci da ake fama da kai
Da yake amsa tanbaya kan halin rashi Tsaro da ke fuskantar kananan hukumomin da yake Wakilta Hon. Jamilu Muhammad
(Dan Zaki, Magayakin Faskari, Sarkin Matasan Abuja)
Ye duk mai bibiyar sa a wannan Sha'ani yasan abin daya faradashi ke nan A majilisa kuma haka yaje yasami Gwamna Dr. Dikko Rada a Matsayin shi na babban shugaban tsaro na jiha kuma yai mai alkawarin hada hanu domin A Shawo kan Matsalar tsaron inji shi


0 Comments